in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a kira taron gaggawa don tattauna batun zaman lafiyar Sudan ta kudu a Khartoum
2018-08-09 09:50:30 cri

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta sanar a jiyar Laraba cewa, ministocin harkokin waje na kasashen mambobin kungiyar raya yankin gabashin Afrika (IGAD) za su yi taron gaggawa a Khartoum don tattauna batutuwan da suka shafi zaman lafiyar Sudan ta kudu.

Ministocin wajen na mambobin IGAD za su gudanar da taron gaggawar ne a Khartoum a yau Alhamis, domin shirin kaddamar da sabon zagayen tattaunawar warware tashin hankalin dake tsakanin bangarorin Sudan ta kudu, in ji Mohamed Abdalla Idris, ministan harkokin wajen Sudan.

Da farko dai an shirya gudanar da sabon zagayen taron tattauna batun rikicin Sudan ta kudun ne a kasar Kenya, amma daga bisani aka sauya zuwa birnin Khartoum.

Idris ya ce, taron zai mayar da hankali ne game da tattauna yadda za'a sanya takamamman lokacin aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar Sudan ta kudun wanda aka kulla a farkon wannan wata a birnin na Khartoum, kana za'a tsara muhimman batutuwan da suka rage ba'a kammala su ba.

A ranar 5 ga watan Agusta ne bangarorin dake yaki da juna a Sudan ta kudu, suka amince da kulla yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe a Khartoum, babban birnin kasar Sudan, game da batun raba madafun iko da kuma tsare tsaren da suka shafi batutuwan tsaro.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China