in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi tir da kisan fararen hula sama da 130 a Mali
2019-03-26 10:22:49 cri

Shugaban hukumar kula da ayyukan tarayyar Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, ya yi tir da kisan kiyashin da aka yi wa fararen hula a Mali.

Sanarwar da aka fitar da yammacin ranar Lahadi, ta ce Moussa Faki Mahamat ya kadu da kisan kiyashin da aka yi a kauyukan Ogossagou da Welingara dake yankin Mopti na tsakaiyar kasar Mali, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 135, ciki har da yara da mata.

Shugaban na hukumar AU, ya yi Allah wadai da mummunan harin kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Ya kuma jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da yi wa wadanda suka raunana fatan samun sauki cikin gaggawa.

Sanarwar ta ce, Moussa Faki Mahamat, ya jadadda bukatar yin dukkan mai yiwuwa wajen zakulo wadanda suka aikata mummunan aikin tare da hukunta su.

Ya ce, abu ne mai muhimmanci, a dauki kwararan matakan kawo karshen irin wadanan tashe-tashen hankula tun daga tushe, yana mai cewa, ci gaba da yinsu, zai kara dagula kokarin da ake yi yanzu, na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China