in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jagoran AU ya yi tir da hari kan sojojin Mali
2019-03-19 10:28:26 cri

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat, ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kaddamar kan wani sansanin sojoji dake kasar Mali.

Faki Mahamat ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, biyowa bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kaddamar kan dakarun sojin kasar Mali a karshen mako, lamarin da ya haddasa kisan sojoji da dama, tare da lalata kayayyakin aiki masu yawa.

Daga nan sai ya bayyana aniyar kungiyar AU, ta ci gaba da baiwa al'umma, da gwamnatin kasar Mali dukkanin goyon baya. Ya ce harin zai ma karawa kungiyar AU karfin halin gudanar da dukkanin ayyukan ta.

Kaza lika babban jami'in na AU, ya jaddada kira ga sassan kasa da kasa, da su fadada gudummawar su, ga yankin da kasar Mali ke ciki, don tabbatar da nasarar ayyukan da ake gudanarwa, na dakile matsalolin tsaro dake addabar yankin yammacin Afirka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China