in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun tabbatar da hallaka mayakan Boko Haram 6
2019-01-05 14:54:00 cri

A jiya Juma'a rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kashe mayakan kungiyar Boko Haram su 6 a yayin wani simame da rundunar ta kai, da nufin tarwatsa maboyar mayakan 'yan ta'addan dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

An hallaka 'yan ta'addan ne bayan da dakarun sojojin suka lalata maboyarsu dake kauyukan Gawa da Boskoro a jihar Borno a ranar Alhamis din da ta gabata, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a Abuja.

Wasu mata uku, da ake zargin mayakan na Boko Haram sun yi garkuwa da su, an kubutar da su a kauyen Boskoro, in ji rundunar sojojin.

Tuni aka kai matan uku da aka kubutar zuwa sansanin tsugunar da 'yan gudun hijira dake Borno.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China