in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin kudin kasashen Afrika suna taron lalibo hanyoyin bunkasa nahiyar a Kamaru
2019-03-05 09:21:18 cri

A ranar Litinin ministocin kudi da kwararru na kasashen Afrika sun bude wani taron kwanaki biyar a Yaounde, babban birnin jamhuriyar Kamaru, domin nazarin hanyoyi da matakan da za'a dauka don bunkasa ci gaban nahiyar.

"Afrika tana da kaso 30 bisa 100 na dukkan arzikin da ake da shi a fadin duniya, amma abin da ake gani a halin yanzu shi ne, talauci dake ci gaba da karuwa. Hakan ya sa dukkannin mambobin kasashen dake kungiyar tarayyar Afrika suka hallara a Kamaru domin tattauna yadda za'a lalibo bakin zaren warware matsalolin, da kuma yadda za'a ciyar da tattalin arzikin nahiyar gaba." Louis Paul Motaze, ministan kudin jamhuriyar Kamaru shi ne ya jagoranci bude taron, ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Taron wanda kwamitin kwararru na musamman na kungiyar tarayyar Afrika da ya shafi batun kudi, da tsare tsaren tattalin arziki da yin hadin gwiwa wato STC ya tsara tare da hadin gwiwar gwamnatin Kamarun.

"A Kamaru muna da tunanin kawo sauye sauye ga tsarin tattalin arziki, saboda shi ne zai haifar da ci gaban albarkatun kasarmu, tare kuma da samar da guraben ayyukan yi, musamman ga matasa. Don haka wannan taro yana da matukar muhimmanci, kuma muna tsammanin cimma matsaya mai yawa da kudurori wadanda za su taimaka mana wajen bunkasa tattalin arzikinmu." in ji Motaze.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China