in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Kamaru ya lashi takwabin sanya kafar wando guda da mayakan 'yan aware muddin ba su mika makamansu ba
2019-01-01 15:08:19 cri

Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru, ya sanar a jiya Litinin da yamma cewa, zai sanya kafar wando guda da mayakan 'yan aware dake yankuna biyu na kasar dake magana da Turancin Ingilishi, muddin suka ki ajiye makamansu, don bin hanyar da ta dace.

Shugaban wanda ya bayyana hakan cikin jawabin da ya saba gabatarwa na karshen shekara ga al'ummar kasar, ya gargadi 'yan aware dake dauke da makamai da su ajiye makaman nasu, idan ba haka ba kuma, gwamnati za ta umarci jami'an tsaro da su karya lagonsu.

Don haka ya ce, gwamnati ta kafa hukumar kwance damara da sake tsugunar da masu dauke da makaman da suke da niyyar mika wuya a yankunan, domin su je su mika makamansu a kokarin kaucewa amfani da tsaurara matakai.

A cewar shugaba Biya, za a hanzarta baiwa kananan yankuna 'yanci tare da inganta tsarin magana da harsuna biyu da bunkasa al'adu, wani bangare cikin matakan da gwamnati ta tsara na kawo karshen tashin hankalin dake faruwa a yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammacin kasar dake fama da rikici.

Jami'an tsaron kasar Kamaru dai na yawaita amfani da kalmar karya lago a matsayin kisa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China