in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar ya yi kira da a kara zage damtse wajen samar da makamashi mai tsafta
2019-03-04 19:40:52 cri

Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar, ya jaddada goyon bayan hadewar yankuna da kara zage damtse don inganta kayayyakin more rayuwa a nahiyar Afirka.

Shugaban ya bayyana haka ne yayin tattauna da shugaban hukumar samar da makamashi da hadin gwiwa ta kasa da kasa Liu Zhenya, inda ya bayyana kudurin kokarin nahiyar na samar da makamashi mai tsafta daga albarkarun da ake iya sabuntawa.

Wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar a jiya Lahadi, ta bayyana goyon bayan kasar na hadewar shiyya da kokarin inganta kayayyakin more rayuwa a Afirka ta hanyar zuba jari kan ayyuka tsakanin kasashe.

Taron ya kuma duba rawar da Masar za ta iya takawa, wajen aiwatar da tsarin samar da makamashi tsakanin kasashen nahiyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China