in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji 16 sun mutu sakamakon harin da aka kai a wani sansanin sojan dake tsakiyar Mali
2019-03-18 14:05:34 cri
Jiya Lahadi, wasu dakaru masu dauke da makamai da ba a san asalinsu ba sun kai hari kan wani sansanin soji dake garin Dioura na yankin Mopti dake tsakiyar kasar Mali, lamarin da ya haddasa rasuwar sojojin kasar a kalla 16.

Bangaren sojojin ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua cewa, wasu dakaru masu dauke da manyan makamai sun kai hari a gabashi da kudancin sansanin sojan da misalin karfe 6 na safe, harin da ya haddasa rasuwar sojoji a kalla 16, yayin da wasu 8 suka bace.

Baya ga haka, bangaren sojan Mali ya tabbatar da cewa, dukkan bangarorin biyu sun yi musayar wuta, lamarin da ya haddasa jin raunuka da hasarar rayuka.

Mazauna wurin sun ce, akwai sojojin Mali 17 zuwa 20 da suka mutu, kuma dakarun sun kwace wasu kayayyakin sansanin soji.

An yi juyin mulkin soja ne a watan Maris na shekarar 2012. A watan Afrilun shekarar 2013, kwamitin sulhun MDD ya zartas da kuduri don kafa tawagar zaman lafiya ta MINUSMA a kasar ta Mali. A watan Mayu na shekarar 2015, gwamnatin kasar ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da neman jituwa tare da wasu kungiyoyin dakaru dake arewacin kasar. A watan Yunin wannan shekara kuma, bangarorin da abun ya shafa sun cimma yarjejeniyar a karshe. Amma, duk da haka, a 'yan shekarun nan an yi ta samun rikici a arewacin kasar, har ma a kwanan nan aka soma tayar da rikici mai zafi, da karuwar hare hare da ake kaiwa a tsakiyar kasar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China