in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fararen hula 37 sun halaka a sakamakon harin da aka kai wani kauyen da ke tsakiyar kasar Mali
2019-01-02 11:10:58 cri
A jiya Talata ne gwamnatin kasar Mali ta fitar da sanarwa, wadda ke cewa wasu dakaru sun kai hari kan wani kauyen da ke tsakiyar kasar, harin da ya halaka fararen hula 'yan kabilar Fulani su 37. Sanarwar ta kuma yi kira ga kabilu daban daban da ke tsakiyar kasar, da su yi hakuri da juna.

A 'yan shekarun nan, rikici ya kara tsananta a tsakanin kabilu daban daban da ke tsakiyar kasar ta Mali, musamman ma a tsakanin 'yan Fulani makiyaya da wasu al'ummu manoma.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China