in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakataren MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a Mali
2019-01-21 09:22:19 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da aka kaiwa sansanin dakarun MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali, harin da ya hallaka sojojin kasar Chadi 10, a kalla wasu 25 kuma suka jikkata.

Mai magana da yawun babban sakataren MDD ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, MDD na kira ga hukumomin kasar Mali da ma kungiyoyi masu dauke da makamai da suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiyar kasar, da su hanzarta zakulo wadanda suka kaddamar da harin domin su girbi abin da suka shuka.

Guterres ya bayyana cewa, hare-hare kan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na iya zama laifukan yaki karkashin dokokin kasa da kasa. Ya kuma nanata cewa, irin wadannan hare-hare, ko kadan ba za su gurgunta kudurin MDD na ci gaba da goyon bayan gwamnati da al'ummar kasar Mali, a kokarin da suke yi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ba.

Sakataren na MDD ya kuma yi amfani da wannan dama wajen mika sakonsa na ta'aziya ga gwamnatin kasar Chadi da ma iyalai da 'yan uwan wadanda suka kwanta dama. Ya kuma yaba wa dakarun tawagar MDD maza da mata dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ta Mali bisa ga kwazo da sadaukar da kan da suka nunawa.

A ranar Lahadi da safe ne dai aka kai hari garin Aguelhok dake yankin Kidal. Sai dai dakarun MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya sun mayar da martani tare da kashe wasu maharan. Rahotanni na cewa, baya ga sojojin kasar 10 da suka rasa rayukansu. A kalla wasu sojoji 25 kuma sun jikkata a harin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China