in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Algeria da Mali suna tattauna hadin gwiwar tsaron kan iyakokinsu
2019-01-24 10:37:55 cri
Kasashen Algeria da Mali sun sha alwashin kara yin hadin gwiwar tsaron kan iyakokin kasashen biyu, a yayin wani taron hadin gwiwa kan al'amurran tsaro da kasashen biyu suka kaddamar a birnin Algiers.

"Matsayin hadin gwiwa da musayar dake tsakanin kasashen biyu yana bukatar a kara karfafa shi, kasancewar yawancin shawarwarin da ake bayarwa a lokacin tarukan shekarun baya ba'a aiwatar da su yadda ya kamata ba," inji sakatare janar na ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Salaheddine Dahmoun, inda ya bayyana hakan a jawabin bude taron tattaunawar.

Dahmoun ya gargadi Algeria da Mali cewa suna shiyyar da ake da barazanar ayyukan ta'addanci da muggan laifuka, musamman matsalar yaduwar makamai da safarar miyagun kwayoyi ta hanayr gamayyar batagari wadanda suka kafa tsarin kawance da kungiyoyin 'yan ta'adda.

Jami'in na Algeria ya kuma bayyana fargabar dawowar ayyukan mayakan 'yan ta'adda daga yankin gabas ta tsakiya, bayan da aka samu galaba kan kungiyar IS a Syria da Iraqi.

Ya ce yin kaura ba bisa ka'ida ba ya kasance wani babban laifi, bayan da bata gari da gamayyar 'yan ta'adda suke amafani da su wajen wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasar Algeria.

A nasa bangaren, sakatare janar na ma'aikatar tsaron al'umma ta Mali, Aser Kamate, ta ce kalubalolin sun shafi dukkan kasashen biyu. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China