in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Filin jirgin saman da Sin ta gina a Habasha ya cika burin kamfanin jirgin saman kasar
2019-01-30 11:07:12 cri

Kamfanin jriga-jirgar jiragen saman kasar Habasha wanda ke sahun gaba a fagen zirga zirgar sufurin jirage a Afrika, ya samu cimma burinsa na zama kamfani mafi girma a Afrika ne sakamakon ayyukan gine ginen kayayyakin more rayuwa da kasar Sin ta gudanar a baya bayan nan.

A ranar Lahadi kamfanin jiragen saman na Habasha ya kaddamar da aikin fadada filin jirgin saman kasa da kasa na Bole dake Addis Ababa, babban birnin kasar, wanda kasar Sin ta samar da kudaden aikin ginawa dalar Amurka miliyan 363.

Sabon filin jirgin saman da aka kaddamar, bankin shigi da fici na kasar Sin ne ya samar da kudaden, kana babban kamfanin gine-gine na kasar Sin ya gudanar da aikin, a yanzu filin jirgin yana da karfin daukar fasinjoji miliyan 22 a shekara, inda ya ninka adadin girman da yake da shi har sau uku, hakan ya bai wa kasar ta Habasha damar zama cibiyar harkokin sufurin jiragen sama mafi girma a nahiyar Afrika.

Firaiministan kasar Habasha Abiy Ahmed, ya bayyana a lokacin kaddamar da filin jirgin saman cewa, "Abin da muka koya a yau daga kaddamar da wannan filin jirgin saman shi ne, akwai gagarumin aiki dake gabanmu."

Kana Ahmed, tare da shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika (AU), Moussa Faki Mahamat, sun kaddamar da wani otel wanda kasar Sin ta gina, wanda ya lashe kudi dala miliyan 65.

Otel din wanda yake da dakin cin abincin Sinawa mafi girma a Afrika, da babban dakin taro mai karfin daukar mutane 2,500, da dakunan baki 373, da wuraren zaman a bakin alfarma, sabon otel din da aka kaddamar mai suna Ethiopian Skylight Hotel, zai taimaka wa kamfanin jirgin saman wajen kyautatuwar harkokin sufurinsa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China