in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Habasha za ta tura babbar tawaga wajen dandalin ziri daya da hanya daya karo na 2
2019-02-15 10:49:48 cri

Gwamnatin kasar Habasha ta ce za ta tura babbar tawaga mai karfi don halartar taron dandalin tattaunawa kan shawarar ziri daya da hanya daya wanda za'a gudanar a watan Afrilu a birnin Beijing, wani jami'in kasar Habasha ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis.

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Nebiat Getachew, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha, ya ce kasashen Habasha da Sin sun jima suna cin moriyar dangantakar dake tsakaninsu, kuma ana fatan kara samun kyautatuwar alakar kasashen biyu a taron na watan Afrilu.

"A watan Janairu, firaiministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya tattauna da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, wanda ya kai ziyarar aiki a kasarmu." in ji kakakin.

"A farkon wannan wata, ministan harkokin wajen Habasha Workneh Gebeyehu ya gudanar da tattaunawa tare da mai taimakawa ministan harkokin wajen Sin, Chen Xiaodong, wanda ya kai ziyara Habasha. Dukkannin tattaunawar ta nuna yadda bangarorin kasashen biyu suke matukar mutunta juna game da dangantakar dake tsakanin Habasha da Sin," Getachew ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China