in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kasashen Afirka su ba da muhimmanci ga kiyaye muhalli
2018-11-27 10:50:05 cri

Masana da masu tsara manufofi sun bayyana cewa, muddin kasashen Afirka na son ci gaban nahiyar, wajibi ne kasashen nahiyar su mayar da hankali ga matakan jure matsalar canjin yanayi da raya tattalin arziki ta hanyar amfani da albarkatun kasa.

Babban darektan cibiyar raya tattalin arzikin kasashe ta hanyar albaratun kasa ta duniya Frank Rijsberman ne ya bayyana hakan yayin taron cibiyar na kwanaki hudu da aka bude a jiya Litinin.

Ya ce, muddin ana son jure tasirin matsalar canjin yanayi, akwai bukatar kasashe su yi kokarin cimma burin samar da makamashin da ake iya sabuntawa 100 bisa 100 domin rage hayaki mai hadari dake gurbata muhalli, da daukar matakan alkinta muhalli wajen amfani da albarkatun kasa don raya tattalin arziki, da amfani da irin shuka mai jure matsalar yanayi.

A cewar masana, karuwar matsalar canjin yanayi, tana yin matukar tasiri ga ci gaban nahiyar Afirka, don haka akwai bukatar a hanzarta musayar bayanai da managartan dabarun samar da ci gaba mai dorewa.

Dandalin da zai gudana daga ranar 26 zuwa 30 ga watan Nuwamban, ya hallara sama da mahalarta 1,000 wadanda suka hada da jami'an gwamnati, da masana a fannin yanayi da muhalli, da masu zuba jari, da wakilan sassa masu zaman kansu. Sauran sun hada da abokan hulda a fannin raya kasa da kungiyoyin gama kai, inda ake sa ran za su yi musayar ra'ayoyi game da amfani da albarkatun kasa wajen raya tattalin arziki da yadda za a jure matsalar canjin yanayi.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China