in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
PLO ta yi Allah wadai da Amurka game da rufe karamin ofishinta a Jerusalem
2019-03-05 11:17:09 cri

Kwamitin zartaswa na kungiya mai fafutukar kwato 'yancin Palastinawa (PLO) ya yi Allah wadai da Amurka bisa rufe karamin ofishin jakadancinta dake Jerusalem.

"Rufe karamin ofishin jakadancin Amurka a Jerusalem da kuma hade shi da ofishin jakadancinta dake Isra'ila ya kasance a matsayin saba yarjejeniyar kasa da kasa wanda ita da kanta Amurkar ce ta jagoranci tsara daftarin yarjejeniyar," wani jami'in PLO shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai.

Sanarwar ta kara da cewa, an gudanar da sauye sauye ga tsarin yarjejeniyar zaman lafiya ta hanyar taron zaman lafiya na kasa da kasa wanda ya samu halartar zaunannun mamobin kasashen dake wakilci a kwamitin sulhun MDD.

Game da batun rufe karamin ofishin jakadancin da Amurkar ta yi, PLO ta yanke shawarar za ta ci gaba da daukar matakai na katse duk wata hulda ko mu'amalar siyasa tsakaninta da kasar Amurka.(Ahmad fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China