in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres zai halarci taron da za a yi a Roma domin mara baya ga UNRWA
2018-03-14 10:26:25 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, zai kai ziyara birnin Roma na Italiya, domin halartar taron mara baya ga hukumar majalisar mai kula da 'yan gudun hijirar Falasdinu.

Kakakin majalisar Stephane Dujarric da ya sanar da tafiyar, ya ce taron da zai gudana gobe Alhamis, na da nufin samun goyon bayan daukacin kasashen duniya wajen kai dauki ga gibin kudin da ya kai kusan dala miliyan 500 da hukumar ke fuskanta, sanadiyyar matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na rage yawan kudin da Amurka ke ba hukumar.

Hukumar ta MDD da ake wa lakabi da UNRWA hukumar ba da agaji ce dake taimakawa 'yan gudun hijirar Falasdinu.

Stephane Dujarric ya ce, shugaban sashen ba da agaji na MDD Mark Lowcock, zai fitar da dala miliyan 30 daga asusun kai daukin gaggawa na majalisar, domin gaggauta taimakawa 'yan gudun hijirar Falasdinu ta hannun hukumar UNRWA. ( Fa'iza Mustapha )

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China