in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin a MDD ya yi kira da a tallafawa shawarwari tsakanin Isra'ila da Falasdinawa
2018-12-19 09:57:45 cri

Jakadan din din din na kasar Sin a MDD Ma Zhaoxu, ya yi kira ga kasashen duniya, da su yi hadin kai wajen tallafawa shawarwarin wanzar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

Ma Zhaoxu, ya yi wannan kira ne a jiya Talata yayin zaman kwamitin tsaron majalissar, yana mai fatan gamayyar kasa da kasa za su sabunta hadin kan su, wajen ganin tattabar da sassan biyu sun koma teburin shawarwari.

Ya ce, akwai bukatar sassan biyu su sadaukar da wasu manufofi na su, domin kaucewa kara dagulewar yanayin dangantakar su, su kai zuciya nesa, tare da kauracewa furta kammalan da ka iya rura wutar rikici, duka dai da nufin samar da yanayi da zai share fagen sake komawa tattaunawa.

Ma Zhaoxu, ya kara da cewa, maida martanin tashin hankali da wani tashin hankalin na daban, ba zai warware wata matsala ba. Don haka kasar Sin ke fatan dukkanin sassan masu ruwa da tsaki za su martaba burin da ake da shi, na samar wa al'ummun dake yankin kariya, da tsaro yadda ya kamata.

Ya ce, matsalolin al'ummar Falasdinu su ne tushen duk wani batu da ke shafar Gabas ta Tsakiya, su ne kuma ke haifar da kalubalen tsaro, da daidaito, da ma gibin ci gaba a daukacin yankin.

Daga nan sai ya ba da shawarar dakatar da dukkanin wasu gine-gine a yankunan da Isra'ila ta yiwa kaka gida, da gaggauta kawar da shingen Isra'ila na yankin Gaza, da kuma daukar matakai na dakile aukawa fararen hula.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China