in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Falasdinu ta yi tir da amincewa dokar nuna wariya da majalisar dokokin Isra'ila ta yi
2018-05-03 11:11:25 cri

Falasdinawa sun yi tir da amincewa dokar nuna wariya da mjalisar dokokin Isra'ila ta yi, wadda ta nemi alkalai su yi amfani da dokokin Yahudawa, inda da can babu doka.

Mambobin majalisar sun kada kuri'ar amincewa da dokar da kuri'u 64 bisa 50, inda dokar ke nufin fadada tasirin dokar Yahudawa kan shari'o'i.

Dokar ta bayyana Isra'ila a matsayin kasar al'ummar Yahudawa, sannan ta ba Yahudawa 'yancin kafa gwamnatinsu a kasarsu.

Har ila yau, dokar na daukar birnin Kudus da ake takaddama kansa, a matsayin babban birnin Isara'ila da kuma harshen Hebrew a matsayin harshenta a hukumance.

Falasdinawa dai sun yi tir da dokar kamar yadda Larabawa mambobin majalisar dokokin Isra'ila suka yi, suna musu mai bayyana ta a matsayin mai nuna wariya.

Wata sanarwa da mamban kungiyar PLO Hanan Ashrwi ya fitar, ta ce dokar na da nufin sahalewa wariyar da Isar'ila ke yi don kawar da Falasdinawa baki daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China