in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan kwangilar kasar Sin sun zamanantar da tsarin gine-gine a Afrika
2019-03-01 10:04:31 cri

Yan kwangilar kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen zamanantar da tsarin gine-gine a nahiyar Afrika.

Shugabar kungiyar masu samar da gidaje ta Afrika (AFRES) Catherine Kariuki, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobin kenya cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, birane a Afrika sun samu gine-gine masu tsayi.

Ta ce, an samu sauyin tsarin gine-ginen ne saboda kudi da fasahohin da Sinawa suka zuba.

Ta kara da cewa, Sinawa sun gabatar da sabuwar fasahar da ta rage lokacin gini ga manyan ayyukan samar da gine-gine.

A cewar kungiyar AFRES, farashin filaye a Afrika musammam tsakiyar birane na ta karuwa cikin sauri, saboda bunkasar tattalin arziki da kaura da ake yi zuwa birane.

Catherine Kariuki, ta ce wannan dalili ne yake karancin filayen gine-gine, inda Sinawa suka taka muhimmiyar rawa wajen ba Afrika damar yin gidajen sama irin na zamani da ba sa bukatar fili mai yawa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China