in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon rahoton MDD ya bayyana karuwar yunwa a Afrika
2019-02-15 09:45:44 cri

Wani sabon rahoton da MDD ta wallafa ya nuna cewa, ana samun karuwar matsalar yunwa a Afrika sakamakon matsin tattalin arziki dake addabar duniya, da matsalar sauyin yanayi sakamakon karuwar tsananin zafi na El Nino, da tashin farashin kayan abinci.

Rahoton ya yi nazari kan yanayin abinci da sinadarai masu gina jiki a Afrika na shekarar 2018, an wallafa shi bisa hadin gwiwar hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD (ECA) da hukumar samar da abinci da bunkasa aikin gona ta MDD (FAO), kuma an bayyana shi a jiya Alhamis a Addis Ababa na kasar Habasha, rahoton ya nuna cewa, matsalar karancin abinci mai gina jiki tana ci gaba da karuwa a Afrika, inda a halin yanzu matsalar ta karu da kashi 20 bisa 100 a fadin nahiyar, sama da sauran sassa na duniya.

A cewar rahoton, akwai mutane kimanin miliyan 821 a duniya, yayin da mutane miliyan 257 ne daga Afrika ke fuskantar wannan barazanar, daga cikin adadin, mutane miliyan 237 suna yankin kudu da hamadar Saharar Afrika, sai kuma wasu mutanen miliyan 20 dake arewacin Afrika.

"Idan an kwatanta da shekarar 2015, mutanen dake fama da karancin abinci mai gina jiki a Afrika sun karu da miliyan 34.5." a cewar rahoton.

Rahoton ya kara da cewa, an samu karuwar kusan rabin mutane masu fama da matsalar karancin abinci mai gina jikin ne daga mutanen yammacin Afrika, yayin da kashi daya bisa uku kuma daga gabashin Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China