Babban darektan cibiyar nazarin manufofin makamashi ta Afirka(ACEP) Benjamin Boakye ya ce, yadda kasar Sin take zuba jari a nahiyar Afirka ya taimaka wajen magance matsalar kayayyakin more rayuwar jama'a na matsakaicin lokaci da nahiyar ke fuskanta.
Haka kuma jarin da take zubawa ya taimaka ga ci gaban nahiyar. Don haka ya shawarci kasashen nahiyar Afirka da su dauki managartan matakai don tabbatar da cewa, an ci gajiyar jarin da kasar ta Sin take zubawa yadda ya kamata, ta yadda nahiyar za ta cimma burinta na samun ci gaba.
Kasar Sin dai tana zuba jari ne a fannonin da suka shafi gina hanyoyin mota, madatsun ruwa, layin dogo wadanda ake ginawa a sassa daban-daban na nahiyar da kudaden da kasar Sin take bayarwa.(Ibrahim)