in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IFC: Jarin Sin na samar da guraben ayyukan yi a Afirka
2019-01-22 20:55:19 cri

Wani jami'in hukumar IFC mai lura da hada hadar kudade ta kasa da kasa a fannin sassa masu zaman kansu a kasashe masu tasowa, ya ce jarin da kasar Sin ke zubawa a kasashen Afirka na bunkasa samar da damammakin aikin yi da ci gaba a nahiyar.

Manajan IFC reshen kasar Kenya, kuma mamba a bankin duniya Manuel Moses, ya bayyana hakan a yayin taro na 7 na manyan jami'an kamfanonin hada hadar cinikayar Afirka. Ya ce akwai bukatar kara mai da hankali a fannin raya sassa masu zaman kan su a kasashe masu tasowa.

Yayin zantawar sa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Nairobi na kasar Kenya, ya ce jarin kasar Sin na taka muhimmiyar rawa, wajen inganta sashen sarrafa hajoji, da na gine gine, da kuma na samar da makamashi.

Mr. Moses ya kara da cewa, sassa masu zaman kan su na Sinawa, ba sa mai da hankali ga kalubale ko hadari dake tattare da kasuwanci a nahiyar Afirka, saboda sun jima suna nazartar nahiyar.

Ya kuma yi hasashen kara samun ci gaba tsakanin Sin da kasashen Afirka, duba da irin hadin gwiwa dake wanzuwa a tsakanin su. Moses ya kara da cewa, Sin na rike da matsayin ta a Afirka, ta hanyar zuba jari dake bunkasa karfin nahiyar na inganta samar da kayayyaki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China