Hukumar kula da tattalin arzikin Afrika ta MDD ta ECA, ta bukaci masu zuba jari na kasashen da ba na Afrika ba, su taka muhimmiyar rawa wajen inganta cinikayya a cikin nahiyar.
Wata sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce masu zuba jari na kasashen waje, za su iya taka muhimmiyar rawa wajen inganta samar da kayayyaki a yankuna da kara yawan cinikayya tsakanin yankunan nahiyar.
Da yake tsokaci game da babbar damar da cinikayya a cikin nahiyar ke da ita ga kamfanonin da ba na nahiyar ba, Daraktan hukumar a yankin gabashin Afrika Andrew Mold, ya ce yarjajeniyar yankin ciniki cikin 'yanci na Afrika ta AfCFTA, za ta inganta harkokin cinikayya a nahiyar da zarar ta fara aiki nan ba da dadewa ba.
Andrew Mold, ya ce yarjejeniyar AfCFTA za ta taimaka wajen karfafa tsarin sarrafa kayayyaki da dunkulewar kungiyoyin nahiyar.
A matsayinta na babbar kasuwar yankin, ana sa ran za ta samar da murya mai karfi na mutane biliyan 1.2, wajen cimma yarjejeniyoyi da wasu kasashe da kungioyoyi a nan gaba. (Fa'iza Mustapha)