in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU na fatan yin hadin gwiwa da Sin karkashin tsarin ciniki maras shinge
2018-03-18 12:45:22 cri
Kungiyar tarayyar Afrika (AU) tana fatan yin aiki tare da kasar Sin da ma sauran abokan hulda dake wajen Afrika kasancewar nahiyar tana kokarin tabbatar da tsarin nan na ciniki marar shinge wato (AfCFTA), wani jami'in kungiyar tarayyar Afrikar ne ya tabbatar da hakan a jiya Asabar.

Kungiyar ta AU tana neman cigaban goyon bayansu kasancewar tana mayar da hankali ne wajen cimma nasarar habaka tattalin arzikin al'ummar nahiyar, Kwesi Quartey, mataimakin shugaban hukumar ta AU, shine ya bayyana hakan a yayin taron kolin AU dake gudana a halin yanzu game da batun tsarin ciniki maras shinge AfCFTA.

Kwesi ya fada a Kigali babban birnin kasar Rwanda cewa, kasar Sin ta kasance babbar aminiyar kasashen Afrika.

Ana saran shugabannin Afrikan zasu sanya hannu kan yarjejeniyar shirin na AfCFTA a lokacin taron kolin, wanda ake kokarin kafa wani yankin kasuwanci marar shinge mafi girma tun bayan kafa tsarin kungiyar kasuwanci ta duniya(WTO), a cewar AU. Tsarin na AfCFTA zai samar da wata kasuwa ga mutane sama da biliyan 1 da miliyan 200 mai karfin ma'aunin tattalin arziki na GDP da ya kai dalar Amurka triliyan 2.5, inji kungiyar ta Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China