in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Buhari ya nanata aniyar dorawa kan nasarorin da ya cimma a wa'adin mulkinsa na biyu
2019-02-28 10:23:16 cri

A jiya Laraba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, zai mayar da hankali wajen rubanya kokari kan nasarorin da ya cimma domin kaiwa kasar zuwa mataki na gaba a tsawon wa'adin mulkinsa na biyu na shekaru hudu.

Da sanyin safiyar ranar Laraba ne dai, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar (INEC), ta ayyana Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar wanda aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Shugaban kasar mai shekaru 76 a duniya, ya ce, aiki tukuru don gina Najeriya zai ci gaba da gudana, ginawa kan zaman lafiyar da aka aza harsashi kansa zai ci gaba, bin doka da oda damammaki ga dukkan 'yan kasa, ya kara da cewa, "ba mu da wata manufa sama da mu gina Najeriya da zuciya daya da dukkan iyawarmu, kuma mu gina kasa wacce al'umma masu tasowa za su yi alfahari da ita."

Taken yakin neman zaben shi ne mataki na gaba a 2019, shugaban na Najeriya dai ya mayar da hankali ne wajen samar da ayyukan dogaro da kai, da gina kayayyakin more rayuwa, da samar da muhallin kasuwanci mai inganci, da tabbatar da tsaro, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China