in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin ta taya shugaba Buhari murnar ci gaba da rike mulki a Najeriya
2019-02-27 19:58:05 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin ta taya shugaban tarayyar Najeriya Muhamadu Buhari murnar ci gaba da rike mulkin kasar tarayyar Najeriya.

Lu Kang ya yi nuni da cewa, Najeriya muhimmiyar aminiyar hadin gwiwa ce ta kasar Sin dake nahiyar Afirka, har kullum kasar Sin tana mai da hankali matuka kan ci gaban alakar dake tsakaninta da Najeriya, haka kuma tana son hada kai da sabuwar gwamnatin Najeriya domin kara karfafa cudanya da hada kai dake tsakanin sassan biyu, ta yadda zai amfani al'ummomin kasashen biyu yadda ya kamata.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China