in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta rufe dukkan iyakokinta gabanin manyan zabukan kasar
2019-02-15 09:12:08 cri

A jiya Alhamis gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin rufe dukkan iyakokin kasar domin samun nasarar gudanar da zaben shugaban kasar da na majalisun dokoki.

Najeriya kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika, za ta gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin kasar ne a gobe Asabar.

A wata sanarwa da ministan cikin gidan kasar Abdulrahman Dambazau ya fitar, ya ce, za'a rufe dukkan iyakokin kasar ne tun daga ranar Juma'a zuwa Lahadi.

A wata sanarwar ta daban, Muhammad Babandede, kwantirola janar na hukumar shigi da fici ta kasar ya bayyana cewa, za'a dakatar da dukkan zirga zirgar jama'a a dukkan iyakokin kasar baki daya a cikin ranakun da za'a gudanar da zaben har zuwa lokacin da za'a sanar da sakamakon zaben.

Haka zalika, hukumar 'yan sandan kasar ma ta sanar da cewa, za'a dakatar da zirga zirgar ababen hawa a ranar Asabar tun da misalin karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma agogin kasar. A cewar kakakin hukumar 'yan sandan Najeriyar Frank Mba, an dauki wannan mataki ne domin gudanar da zabukan cikin nasara.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China