in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu a turmutsitsin yakin neman zabe a Nijeriya ya karu zuwa 15
2019-02-14 09:54:41 cri

Adadin wadanda suka mutu a turmutsitsin yakin neman zabe ranar Talata a jihar Rivers dake kudancin Nijeriya, ya karu zuwa 15.

Kakakin asibitin koyarwa na birnin Fatakwal Kem Daniel-Elebiga, ya bayyan cikin wata sanarwa cewa, alkaluma daga sashen ba da agajin gaggawa na asibitin sun nuna cewa, gawarwaki 15 aka kai, wadanda suka hada da maza 3 da mata 12.

Ya kara da cewa, mutane 12 da suka raunana kuma sun samu kulawa kan kari, inda har aka sallami 3 daga cikinsu.

Turmutsitsin ya auku ne ranar Talata a filin wasa na Fatakwal, babban birnin jihar Rivers, yayin da magoya bayan jam'iyyar APC mai mulkin kasar, ke kokarin barin wurin, bayan gangamin yakin neman zaben Shugaba Muhammadu Buhari. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China