in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
OCHA: Yawan masu fama da barazanar yunwa a kahon Afirka ya kai miliyan 22.4
2018-10-04 15:37:26 cri
A jiya Laraba ne ofishin MDD mai lura da ayyukan jin kai ko OCHA a takaice, ya ce adadin mutane dake fuskantar barazanar yunwa a yankin kahon Afirka ya kai mutum miliyan 22.4.

Cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, ofishin na OCHA ya ce a kasar Kenya, adadin mutanen dake matukar bukatar agajin abinci ya kai mutum dubu dari 7, kana a kasar Somaliya adadin ya kai mutum miliyan 1.6, yayin da a Sudan ta kudu ya kai mutum miliyan 6.1.

Sauran kasashen dake fuskantar barazanar kamfar abinci a yankin su ne Habasha, wadda al'ummunta dake bukatar tallafin abinci suka kai miliyan 7.9, yayin da kuma 'yan kasar Sudan dake cikin wannan bukata, suka kai mutum miliyan 6.2.

Ofishin na OCHA ya kara da cewa, yake-yake na basasa, na kara rura wutar wannan matsala a Sudan ta kudu. Sai dai kuma a daya hannun, tallafin jin kai, da wadataccen ruwan sama da aka samu a Somaliya, ya rage adadin masu fama da karanci abinci a kasar.

Bugu da kari, OCHA ya ce baya ga karancin abinci, yankin na kahon Afirka, na fuskantar matsalar 'yan gudun hijira, wadanda tashe tashen hankula suka raba da muhallansu, musamman a yankunan kasashen Habasha, da Somaliya, da kuma Sudan ta Kudu. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China