in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an kasashen Asiya da Afrika suna samun horo game da adana hatsi
2017-10-25 11:04:05 cri

Jiya Talata a birnin Chengdu na lardin Sichuan, jami'ai 15 daga kasashen Nijer, Uganda, Tanzaniya da sauran kasashen Asiya da Afirka 3 sun fara samun horo game da yadda ake adana hatsi.

Hukumar harkokin abinci ta kasar Sin da ofishin hukumar tsara shiri kan abinci ta MDD a nan kasar Sin su ne suka shirya ba da horon cikin hadin gwiwa, a kokarin inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, da taimaka musu wajen kyautata fasahar adana hatsi da rage asara, da kara sanin yadda manoma suke adana hatsi da rage asara yadda ya kamata, tare kuma da kyautata yadda ake sarrafa hatsi, da inganta huldar dake tsakanin manoma da 'yan kasuwa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China