in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sudan ya ayyana dokar ta baci na shekara guda da rusa majalisar zartaswar kasar
2019-02-24 15:07:43 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a ranar Juma'a ya ayyana dokar ta baci na shekara guda a dukkan fadin kasar ta Sudan tare da rusa gwamnatin tsakiya da gwamnatocin jihohin kasar bayan da kasar ta shafe sama da watanni biyu kasar na fuskantar zanga-zanga.

Wannan mataki ya biyo bayan wani muhimmin taro ne da al-Bashir ya gudanar a ranar Juma'a, tare da mambobin kwamitin dake jagorancin tattaunawar kasar, da gwamnonin jahohi da manyan shugabannin jam'iyyar dake mulkin kasar.

Al-Bashir ya ce, sabuwar majalisar ministocin kasar za ta dauki kwararan matakai kan tattalin arzikin kasar, ya kara da cewa, ya umarci kwamitin kolin dake tafiyar da harkokin mulkin kasar da ya ci gaba da tattaunawa har a cimma gaci wajen warware tarzomar kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China