in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron dandalin ma'adanai na kasa da kasa a Sudan
2019-02-19 10:47:25 cri
Jiya Litinin aka bude taron dandali da nune nunen ma'adanai karo na 4 a Khartoum, babban birnin kasar Sudan, inda ya samu halartar wakilai daga kasashe sama da 40.

"Wannan taron an bude shi ne a wani yanayi mai cike da sarkakiya a matakan shiyya da kasa da kasa," inji Firaministan kasar Sudan Mutaz Musa, a lokacin da ya jagoranci bikin bude taron.

Yanayin kalubalolin da ake ciki yana bukatar a dauki matakai na hadin gwiwa a fannin ma'adanai, domin samar da ingantaccen yanayi da kuma samar da muhimman kayayakin more rayuwa da ake bukata, injishi.

Musa ya kara jaddada aniyar kasar Sudan wajen bude kofarta ga al'ummar kasashen waje dake da sha'awar zuba jari a fannin ma'adanan kasar ta Sudan.

Taron dandalin, wanda aka tsara gudanarwa tsakanin ranaku 18 zuwa 20 ga watan Fabrairu, za'a tattauna batutuwa da suka shafi ma'adanai wanda 'yan kasar Sudan da kuma masanan kasashen waje suka gabatar.

Sudan tana kokarin mayar da zinare a matsayin babbar hanyar samun kudaden shigarta daga kasashen waje, bayan da ta yi hasarar kashi uku bisa hudu na kudaden shigarta daga albarkatun mai, tun bayan ballewar yankin Sudan ta kudu daga kasar a shekarar 2011.

A shekatat 2018, Sudan ta samar da sama da ton 110 na zinare kuma ta zama kasar dake sahun gaba wajen samar da zinare a Afrika. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China