Mataimakin firaministan kasar Sin Hu Chunhua ya bukaci a yi cikakken sanya ido wajen aiwatar da shirin yaki da fatara domin samun nasarar aikin kawar da kangin fatara a kasar.
Hu, wanda shi ne shugaban ofishin kula da shirin yaki da fatara da samun bunkasuwa na majalisar kolin kasar Sin, ya yi wannan kiran ne a lokacin wata ziyarar kwanaki uku da ya kaddamar a lardin Hebei dake arewacin kasar Sin wanda ya kammala ziyarar a jiya Talata.
Hu ya ce, wajibi ne hukumomin kananan yankuna su sanya ido a ko da yaushe kan ayyukan rage radadin talaucin, kana su kara kaimi wajen daukar matakan da za su tabbatar da ganin ana aiwatar da aikin yaki da fatara yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)