in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da kiyaye da aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran a dukkan fannoni
2018-05-21 19:52:57 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen ksar Sin Lu Kang ya ba da tabbacin cewa, kasarsa za ta halarci taron hadadden kwamiti game da yarjejeniyar batun nukiliyar Iran a dukkan fannoni.

Lu ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Litinin. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye tare da martaba yarjejeniyar.

Rahotanni na cewa, a ranar 25 ga wannan wata ne kasashen Iran, Sin, Rasha, Faransa, Jamus da kuma Burtaniya za su shirya wani taron hadadden kwamiti game da yarjejeniyar nukiliyar Iran a dukkan fannoni ne. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Seyed Abbas Araqchi ya ce, a yayin taron za a tattauna tasirin da janyewar Amurka ta yi daga yarjejeniyar, da kuma yadda bangarori daban daban da batun ya shafa za su ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China