in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu za ta koyi dabarun raya yankunan musamman na tattalin arziki daga kasar Sin
2019-02-19 10:28:36 cri
Shugaban lardin Gauteng na kasar Afrika ta Kudu David Makhura, ya sanar a jiya Litinin cewa lardinsa zai koyi dabarun kasar Sin na raya yankunan tattalin arziki na musamman domin bunkasa tattalin arziki da samar da guraben ayyukan yi.

Da yake jawabi game da halin da lardin ke ciki a Johannesburg, Makhura ya ce, za su yi koyi da kasar Sin wajen kafa yankunan tattalin arziki na musamman domin magance manyan kalubalolin dake damun kasar.

Ya ce za su kara azama domin daukar kwararan matakai wajen ciyar da yankin kasarsu gaba, inda za su mayar da shi wani yankin tattalin arziki na musamman.

"Wannan shi ne misalin irin manufar raya yankin Hainan, wani tsibiri ne dake kasar Sin, inda ya koma yankin musamman na tattalin arziki tun bayan da kasar Sin ta aiwatar da shirinta na yin gyare gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, a yanzu Sin ta zama kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya." Lardin Hainan wani yankin mausamman ne na tattalin atziki, inji Makhura.

Bisa alkaluman jarin kasashen waje na kai tsaye ko kuma fDi a takaice, wani sashe na musamman ne na binciken harkokin masana'antu na jaridar Financial Times, an ce, lardin Gauteng shi ne yanki na 7 mafi karfin tattalin arziki a Afrika. A shekaru biyar din da suka gabata, yankin ya janyo hankalin jarin kai tsaye na kasashen waje wanda ya kai na dalar Amurka biliyan 14.2 da kuma samar da guraben ayyukan yi kimanin 30,000.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China