in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin fasinjojin da CAAC ta yi jigila tsakanin kasa da kasa a Janairu ya zarta miliyan 6
2019-02-15 10:53:21 cri

A ranar 13 ga wata, hukumar zirga-zirgar jiragen saman fasinjan kasar Sin wato CAAC a takaice, ta fitar da wani rahoto game da aikin da ta yi a cikin watan Janairun bana, inda ta bayyana cewa, a cikin watan Janairun, gaba daya adadin fasinjojin da aka yi jigilarsu da jiragen sama a fadin kasar Sin ya kai miliyan 53 da dubu 413, adadin da ya karu da kaso 14.9 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, a cikin su, adadin fasinjojin da aka yi jigilar tsakanin kasar Sin da kasashen ketare ya zarta miliyan 6, wanda ya fi yawa a tarihi, wato ya kai miliyan 6 da dubu 75, adadin da ya karu da kaso 22.9 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.

Kana adadin jiragen saman fasinjan da suka tashi daga filayen saukar jirgin saman fadin kasar ya kai dubu 498 da 486, wato ko wace rana dubu 16 da 81 suka tashi a filayen, adadin da ya karu da kaso 11.05 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Ban da haka kuma, wadanda suka tashi sama cikin lokaci sun kai kaso 83.6 bisa dari, haka kuma adadin da ya karu da kaso 1.57 bisa dari bisa bara.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China