in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude dandalin raya hanyoyin jiragen sama na duniya a Guangzhou
2018-09-17 10:37:50 cri
Mataimakin darektan hukumar kula da harkokin zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Sin Wang Zhiqing ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da kasancewa daya daga cikin kasuwannin jiragen sama dake saurin bunkasa, saboda yadda ake kara bukatar zirga-zirgar jiragen sama.

Darekta Wang ya bayyana hakan ne yayin taron dandalin raya harkokin zirga-zirgar jiragen sama na duniya karo na 24 da aka bude jiya Lahadi a birnin Guagzhou na kasar Sin.

A shekarar da ta gabata kasar Sin ta bude sabbin hanyoyin zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa guda 382, adadin da ya karu zuwa 1,634, wanda ya nika na shekarar 2015. Kana a shekarar da ta gabata an yi tafiye-tafiye miliyan 550 ta jiragen sama a kasar, wanda ya kai kaso 16.3 cikin 100 na adadin duniya baki daya.

A jawabinsa shugaban kamfanin zirga-zirgar jiragen sama a kasar Habasha Tewolde GebreMariam ya ce, suna fatan bunkasa kasuwar zirga-zirgar jiragen sama a kasar Sin, yayin da harkokin cinikayya da zuba jari da na yawon shakatawa tsakanin Sin da kasashen Afirka ke bunkasa.

Ya kara da cewa, adadin fasinjoji tsakanin kasar Sin da kasashern Afirka zai ci gaba da karuwa da kaso 20 cikin 100 a kowace shekara. Kana kamfanin na shirin kaddamar da sabbin hanyoyin jiragen sama zuwa Shenzhen da wasu karin jiragen da za su rika zuwa Guangzhou da sauran birane dake kasar Sin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China