in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan takarar shugabancin Nijeriya su sabunta alkawarinsu na tabbatar da zaben kasar ya gudana lami lafiya
2019-02-14 09:50:03 cri

Yan takarar shugabancin Nijeriya, sun sabunta alkawarinsu na tabbatar da zaben kasar ya gudana cikin lumana, yayin da kasar ke tunkarar babban zabenta, inda za a fara da zaben shugaban kasa a ranar Asabar, 16 ga wata.

Rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar karo na 2, tun bayan wanda aka yi a watan Disamban shekarar 2018, ya gudana ne jiya, a Abuja babban birnin kasar.

Shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari, wanda yake neman zarcewa kan shugabancin kasar a karo na 2 karkashin jam'iyyar APC da 'dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP wato Atiku Abubakar, na daga cikin 'yan takarar da suka halarci taron.

Sanya hannu kan yarjejeniyar na nufin, 'yan takarar da jam'iyyunsu za su kaucewa furta kalaman kiyayya da batanci da yada labaran bogi da duk wani abu da ka iya haifar da rikicin siyasa da zamantakewa a kasar.

Yan takarar sun kuma yarda za su amince da sakamakon zaben da hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC za ta ayyana.

Da yake jawabi, shugaba Buhari ya bayyana gamsuwa game da yadda 'yan takara ke tafiyar da gangamin yakin neman zabe a fadin kasar, yana mai kira ga matasa su kauracewa tada rikici yayin da kuma bayan zaben.

A nasa bangaren, Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa, ya yi kira ga INEC da hukumomin tsaro da aka dorawa nauyin tabbatar da zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, su kamanta gaskiya da adalci yayin aikin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China