in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan cinikin wajen Sin ya karu da kaso 8.7 bisa dari cikin Janairu
2019-02-14 13:54:43 cri

Alkaluma daga hukumar kwastam ta kasar Sin, sun ce cinikin kayayyakin dake tsakanin kasar da kasashen ketare ya karu da kaso 8.7 bisa dari a cikin watan Janairun bana, inda ya kai yuan triliyan 2.73 kwatankwacin dala biliyan 395.98.

Cinikayya tsakanin kasar Sin da kasashen Turai ya karu da kaso 17.6 bisa dari, inda tsakaninta da kasashen kudu maso gabashin Asiya ya karu da kaso 7.8 bisa dari, yayin da cinikayya tsakaninta da Japan ya karu da kaso 6.5 bisa dari.

Har ila yau, kasuwanci tsakaninta da kasashen dake cikin shawarar ziri daya da hanya daya, ya habaka har ya zarce matsakaicin mataki, inda darajarsa ta kai yuan biliyan 770.8, wanda ya karu da kaso 11.5 bisa dari a kan na makamancin lokacin a bara.

Fitar da kayayyakin kasar Sin zuwa Amurka kuwa ya karu da kaso 1.9 bisa dari, yayin da kayayyakin da ake shigar da su daga Amurkar ya sauka da kaso 38.6 bisa dari.

Bangarori masu zaman kansu sun taka gagarumar rawa, inda suka mamaye kaso 42.3 bisa dari na jimilar ci gaban kasuwanci da aka samu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China