Kididdigar ta cewa, yawan karuwar cinikin da aka yi ta dandalin yanar gizo na kamfanin Alibaba a yankunan karkarar kasar Sin ya kai kashi 23.8 bisa dari a shekarar da ta shude, adadin da ya zarce na wasu manyan biranen kasar Sin da kashi 4.5 bisa dari, ciki har da Beijing da Shanghai da Guangzhou da kuma Shenzhen.
Rahoton ya bayyana cewa, adadin yawan bukatar da ake da ita a yankunan karkara zai kasance a matsayin wata muhimmiyar hanyar dake kara ci gaba sakamakon bunkasuwar hanyoyin ciniki na zamani, da karin damammakin amfani da shafukan Intanet da saurin samar da kayayyakin da ake bukata.
Har wa yau, yanar gizo za ta rage gibin dake kasancewa tsakanin yankuna masu ci gaban tattalin arziki dake gabashin kasar Sin da yankunan karkara marasa ci gaba na kasar.(Murtala Zhang)