in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadarin jirgi ya halaka mutane 5 a Kenya
2019-02-13 19:32:56 cri

Wasu baki 'yan kasashe waje guda biyar sun gamu da ajalinsu, lokacin da wani karamin jirgin sama da suke ciki ya yi hadari a yankin Kericho dake arewa maso yammacin kasar Kenya a Larabar nan.

Kwamandan rundunar 'yan sandan yankin Edward Mwamburi, ya bayyana cewa, mutanen da suka mutu, duk 'yan kasashen waje ne dake kan hanyarsu ta zuwa Lodwar daga shahararren wurin yawon shakatawar nan na Masai Mara, lokacin da karamin jirgin da suke ciki ya gamu da matsalar inji ya kuma fadi a yankin Kamwingi dake garin Londiani na yankin Kericho.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa, jirgin ya gamu da matsala tun ma kafin ya bugi wata bishiya. An kuma yi imanin cewa, fasinjojin dake cikin jirgin 'yan yawon bude ido da matukin jirgin.

Har yanzu dai ba a kai ga gano kasashen da mutanen suka fito ba, ana kuma gudanar da bincike don gano musabbin hadarin.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China