A jiya Laraba Kenya ta dakatar da neman karamin jirgin saman da ya bace a karo na biyu sakamakon rashin kyawun yanayi, jirgin wanda ya yi batan dabo a tsakiyar Kenya a ranar Talata.
Kwamishina mai kula da yankin Nyandarua, Boaz Cherutich, ya ce tawagar masu binciken jirgin suna fuskantar kalubalen rashin kyawun yanayi a dajin Aberdares, inda daga wajen ne aka daina jin duriyar jirgin.
Karamin jirgin saman, samfurin Fly-SAX, yana dauke da fasinjoji 8 da ma'aikatan jirgin guda 2, kamfanin jirgin ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a daren Talata. Hanyoyin tattaunawa da jirgin sun katse ne da yammacin ranar Talata a yayin da jirgin ke kan hanyarsa daga garin Kitale na arewa maso yammacin Kenya zuwa birnin Nairobi.(Ahmad Fagam)