in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana shirin kaddamar da shirin samar da hidima ga tsofaffi ta Intanet
2019-02-13 19:28:26 cri

Hukumar kula da harkokin kiwon lafiya ta kasar Sin ta sanar da kananan hukumomin kula da harkokin lafiya dake kasar cewa, daga watan Fabrairun da muke ciki zuwa watan Disamba, kasar za ta kaddamar da wani shirin samar da hidima ga tsofaffi ta Intanet.

Karkashin wannan shiri, cibiyoyin da aka amince da su, za su iya tura ma'aikatansu na jinya zuwa al'ummomi ko gidaje domin kula da marasa lafiya da suka tsofa ko da ba sa iya tafiya sakamakon wata cuta da suka fama da ita.

A karkashin wannan shiri na gwaji, an zabi larduna guda 6 dake sassan kasar da suka hada da Beijing da Tianjin da Shanghai da Jiangsu da Zhejiang da Guangdong. Haka kuma sauran yankunan za su iya zabar wasu birane ko yankuna domin shiga cikin wannan shirin.

Shirin dai yana bukatar ma'aikatan jinya da za su shiga wannan aiki su kasance suna da kwarewar aiki na a kalla shekaru biyar. Za kuma a adana dukkan bayanan da aka tattara yayin da ake aikin ba da wannan hidima domin cika ka'idojin da ake bukata. Bugu da kari, an tanadi na'urorin sanin wurare da wata kararrawar kariya domin tabbatar da tsaron lafiyar ma'aikatan jinyar dake gudanar da wannan aiki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China