in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na sa ran ganin an kiyaye hakkokin mutane masu bukata ta musammam
2018-12-04 09:56:53 cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga al'ummomin kasa da kasa, da su yi aiki tare wajen samar da duniya mai adalci da karko da kuma tafiya tare da kowa, wadda za a rika kiyaye hakkokin mutane masu bukata ta musammam.

A sakonsa na ranar tunawa da masu bukata ta musammam ta duniya, Antonio Guterres ya ce, sama da mutane biliyan 1 a duniya ne ke fama da wani nau'i na nakasa, kuma a al'ummomi da dama, a kan nuna musu wariya da tsangwama.

Ya ce, muradun ci gaba masu dorewa da ake son cimmawa ya zuwa shekarar 2030 na da burin rage bambanci da inganta damawa da kowa cikin harkokin zamantakewa da tattalin arziki da siyasa, ciki har da masu bukata ta musammam.

Ya ce, hakan na nufin, aiwatar da kudurin MDD kan hakkokin masu bukata ta musammam ta kowacce fuska a kuma dukkan kasashe. Har ila yau yana da nufin sanya bukatu da damuwar masu bukata ta musammam cikin manufofi da dabarun gwamnati. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China