Kididdiga daga hukumar lafiya ta kasar ta nuna cewa, a bana, ba a samu cutar karancin sinadarin iodine ba a kaso 94.2 na yankunan kasar, haka zalika, an takaita barkewar cutar Keshan a kaso 94.2 na yankunan da a baya ake yawan samun ta, yayin da kuma babu cutar Kashin Beck baki daya a kaso 95.4 na yankunan da a baya aka fi samu.
Karewa da magance cututtuka sun kasance muhimman bangare na kokarin kasar na yaki da talauci. A cewar kididdigar, daga cikin gundumomi 832 a matakin kasa, da talauci ya yi wa katutu, 831 na fama da karancin sinadarin iodine, yayin da 584 ke fama da barazanar sauran cututtuka.
Bisa jadawalin da aka tsara na karewa da magance irin wadancan cutuka da aka fitar a bara, kasar Sin za ta himmantu wajen kawar da cutuka irinsu na karancin iodine da cutar Keshan da Kashin-Beck da kuma takaita cutuka irin na su gubar sinadarin fluorine. (Fa'iza Msutapha)