in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane da dama sun mutu a hadarin tankar mai a Najeriya
2019-01-13 16:05:53 cri
Mutane da dama sun rasa rayukansu a sanadiyyar gobarar wata tankar mai a ranar Juma'a akan babbar hanyar Calabar zuwa Odukpani dake jahar Cross River a kudancin kasar.

Lamarin dai ya faru ne bayan da tankar man ta fadi, a yayin da mazauna kusa da inda lamarin ya faru suke ta kokarin kwasar man dake Malala.

An samu tashin gobara ne lokacin da masu kwasar man ke amfani da wasu kwanukan daukar mai na karfe.

Hadarin ya yi sanadiyyar kashe rayukan sama da mutane 20, kamar yadda wani da ya ganewa idonsa ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Gwamna Ben Ayade na jahar ya gargadi mazauna yankin da su guji jefa kansu cikin hadari, ya kara da cewa, ma'aikatar yada labarai da wayar da kan jama'a za ta fara aikin gangamin wayar da kan jama'a game da wannan batu.

Chidiebere Nkwonta, kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa dake jahar, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tankar ta fadi ne a gefen hanya.

"Muna zaton hadarin ya faru ne sakamakon karya dokokin tuki daga bangaren direban. Direban ya dan samu raunuka a lokacin da jami'an hukumarmu suka ziyarci inda lamarin ya faru," in ji shi.

Ya shedawa Xinhua cewa, sun yi ta kokarin tabbatar da ganin an cigaba da zirga zirga cikin tsanaki don kiyaye lafiyar al'umma a yankin da hadarin ya afku.

"Sai dai abin takaici shi ne, cikin dare mutane suka dinga kai-kawo a wajen domin kwasar man, daga bisani aka samu tashin gobarar wanda ta haddasa hasarar rayuka," in ji jami'in.

Jami'in ya gargadi mutane da su guji zuwa inda aka samu hadarin tankar mai domin kwasar albarkatun man, don kare lafiyarsu.

Wasu da suka samu raunuka a hadarin an garzaya da su zuwa asibitin koyarwa na jami'ar Calabar domin duba lafiyarsu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China