An cimma yarjejeniyar ne bayan da aka amincewa Iran da kada ta rage danyen man da take hakowa sakamakon takunkumin da Amurka ta kakaba mata.
Yawan man da Amurka ke hakowa, wanda ya karu da ganga miliyan 2.5 na danyen man tun a farkon shekarar 2016 zuwa ganga miliyan 11.7 a kowace rana, ya haifarwa kungiyar ta OPEC da sauran kasashen dake samar da danyen mai damuwa game da takara a kasuwannin mai na duniya.
Matakin rage hako man da kasashen na OPEC da wadanda ba na OPEC ba suka dauka, ya zo ne a daidai lokacin da aka samu faduwar farashin man da kaso 30 bisa 100 cikin watanni biyun da suka gabata a kasuwannin mai na duniya.