in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bukaci a dauki ingantattun matakan bai daya wajen yaki da ta'addanci
2019-02-12 11:40:29 cri

Jiya Litinin, wani wakilin kasar Sin ya bukaci a dauki ingantattun matakai na bai daya wajen yaki da ayyukan ta'addanci

Wu Haitao, mataimakin wakilin din din din na kasar Sin a MDD, ya bayyana hakan ne ga kwamitin sulhun MDDr, cewar domin kawar da ayyukan ta'addanci, wajibi ne dukkan kasashen duniya su rungumi ingantaccen tsari na bai daya da kuma amfani da tsarin ba sani ba sabo.

Mista Wu ya kara da cewa, yaki da ayyukan ta'addanci na kasa da kasa wajibi ne ya dace da manufofi da kuma yarjejeniyar dokoki na MDD, da suka kunshi mutunta 'yancin kiyaye ikon kasashe, da baiwa kasa ikon wakilci, da bayar da cikakkiyar dama ga rawar da kasa za ta taka a tsarin ayyukan kwamitin sulhun MDD, da kuma cikakken aiwatar da muhimman kudurorin kwamitin sulhun da kuma dokokin yaki da ayyukan ta'addanci na kasa da kasa.

Ban da wannan, Wu ya ce, ta'addanci babban makiyi ne na bil adama, kuma babu wata kasa a duniya da za ta iya magance matsalar ita kadai. Wajibi ne al'ummar kasa da kasa su rungumi tsarin gina makomar bil adama ta bai daya, da rungumar tsarin hadin gwiwa, da tabbatar da hadin kai da yin aiki tare wajen yakar barazanar ayyukan ta'addanci.

Wu ya bukaci kasashe mambobin MDD da su dauki tsauraran matakan dakile hanyoyin yaduwar ayyukan ta'addanci, kana su shawo kan dukkan wasu alamun yaduwar ta'addanci da abubuwan dake haifar da matsalar.

Kamata ya yi kasashen duniya su tallafawa takwarorinsu wajen cimma nasarar bunkasuwar tattalin arziki da cigaban zamantakewar al'umma, da taimakawa hanyoyin warware matsalolin da ake takaddama kansu ta hanyar matakan siyasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China