in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin kasuwancin kasar Sin na da kyau a lokacin bikin bazara
2019-02-08 16:05:18 cri

Lokacin bikin bazara wani muhimmin lokaci ne mai cike da murna da jin dadi ga Sinawa, inda su kan yi haduwar iyalai, da yawon shakatawa, gami da sayayya. A shekarun baya, yanayin zaman rayuwar Sinawa mazauna birane da kauyuka na kara samun kyautatuwa, lamarin da ya sanya ake sayen karin kayayyaki, da biyan karin kudi ga hidimomin da aka samar, a lokacin bikin bazara.

Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, a lokacin bikin bazara na bara, Sinawa sun kashe kudin Sin RMB Yuan biliyan 926 wajen sayen kayayyaki da cin abinci, adadin da ya karu da kashi 10.2% bisa makamancin lokacin shekarar 2017. Sa'an nan a wannan shekarar da muke ciki, ana sa ran ganin jimillar ta zarce Yuan biliyan 1000. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China