in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana share fagen karbar Sinawa masu yawon shakatawa a kasashe daban daban
2019-02-04 13:21:16 cri

Tun daga yau Litinin ne aka fara hutun bikin bazara a nan kasar Sin, kana wani rahoton da aka gabatar ya yi hasashen cewa, a yayin wannan hutu na kwanaki 7, Sinawa kimanin miliyan 400 za su yi yawon shakatawa, kana a cikinsu kusan miliyan 7 za su tafi kasashen waje.

Don janyo hankalin Sinawa masu yawon bude ido, kasashe daban daban sun gabatar da matakai don samar musu da sauki, gami da taya su murnar bikinsu.

A kasar Thailand, an baiwa Sinawa damar samun izinin shiga kasar cikin sauki, kuma ba tare da biyan kudi ba. Haka kuma, an rataya alamun taya murnar bikin bazara a manyan cibiyoyin kasuwancin dake birnin Bankok.

A kasar Japan kuwa, an dauki ma'aikata Sinawa aiki a kasuwannin kasar, wadanda za su iya ba da hidima ga 'yan kasar Sin cikin sauki. Haka zalika, yau da dare, za a yi amfani da manyan fitilu 36 domin canza launin babban ginin nan na "Hasumiyar Tokyo" zuwa launin ja, don taya Sinawa murnar bikin bazara na kasar Sin, ta la'akari da yadda Sinawa ke yawan amfani da abubuwa masu launin ja wajen taya murnar bikin na gargajiyar kasar Sin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China